Fursunoni bakwai sun kammala karatun digiri a gidan yari na Kuje

(kuje)

Cibiyar gyaran hali ta Kuje da ke Abuja ta bayyana cewa fursunoni bakwai (7) daga cikin waɗanda ke tsare a wurin sun kammala karatun su, bayan gudanar da shirin ilimi da horo da ake yi a cikin gidan yari.

Wannan ci gaba, a cewar hukumar kula da gidajen gyaran hali ta Najeriya, na daga cikin yunkurin gwamnati na gyara halin fursunoni ta hanyar ba su damar ilimi da horo domin su zama masu amfani wa kansu da al’umma bayan fitowarsu daga gidan yari.

Shugaban cibiyar, ya bayyana cewa, shirin ya ƙunshi ilimi, sana’o’in hannu, da koyar da dabarun rayuwa, domin tabbatar da cewa waɗanda suka kammala fursunanci za su iya dogaro da kansu.

Ya ce wannan mataki yana nuna cewa, gidajen gyaran hali ba wai wurin ɗaurewa ba ne kawai, har ma wurin gyara da canza rayuwa.

Hukumar ta kuma tabbatar da cewa za ta ci gaba da haɗa kai da hukumomin ilimi da ƙungiyoyi masu zaman kansu domin tallafawa irin waɗannan shirye-shirye a sauran cibiyoyin gyaran hali na ƙasar.

Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.


Post a Comment

0 Comments