Sojojin Najeriya sun kashe ’yan ta’adda 17, sun kama 85, sun ceci mutum 10 Da akayi Garkuwa da Su.

(Nigerian troops)

Dakarun sojin Najeriya sun bayyana cewa sun kashe ’yan ta’adda 17, sun kuma kama mutane 85 da ake zargi da hannu a ta’addanci da sauran laifuka a faɗin ƙasar.

 Haka zalika kuma, sun ceci mutum 10 daga hannun masu garkuwa a cikin kwanaki 48 da suka gabata.

Hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ce ta tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar a yau, inda ta ce an gudanar da jerin hare-hare da bincike a jihohi daban-daban na ƙasar, ciki har da Borno, Adamawa, Zamfara, Sokoto, Plateau, Nasarawa, Benue, Rivers, da Delta.

A cewar sanarwar, rundunar Operation Hadin Kai da ke Arewa maso gabas ta yi artabu da ’yan ta’adda a Borno da Adamawa, inda ta kwato makamai da kayan abinci da ake kaiwa maboyar ’yan Boko Haram da ISWAP.

Haka kuma, Operation Hadarin Daji a Arewa maso yamma ta kama masu safarar miyagun ƙwayoyi da masu bawa yan bindiga bayanan a Zamfara da Sokoto.

A bangaren Arewa ta tsakiya kuma, Operation Safe Haven ta samu nasarar ceton mutum ɗaya daga hannun masu garkuwa da mutane a Plateau, tare da kama wasu a Nasarawa da Benue.

A yankin Kudu, Operation Delta Safe ta fatattaki masu fasa bututun mai, inda ta kama jirgin ruwa ɗauke da lita 840 na man fetur da aka safara ba bisa ƙa’ida ba.

Rundunar ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da kai farmaki kan masu aikata laifuka har sai an tabbatar da zaman lafiya a ƙasar baki ɗaya.

Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.

(Dailynigerian)

Post a Comment

0 Comments