Daya daga Cikin Tsofaffin Gwamnonin kasar nan na Fuskantar Bincike bisa Zargin hadin baki a Juyin Mulkin da aka shirya

(cristopher musa)

Rahotanni daga majiyoyi masu tushe sun bayyana cewa wani tsohon gwamna daga yankin kuduncin Najeriya na Fuskantar bincike bisa zargin cewa yana da hannu a wani yunkurin juyin mulki da aka ce an shirya aiwatarwa a ranar 25 ga Oktoba, 2025.

Majiyoyin sun bayyana cewa ana zargin tsohon gwamnan da taimakawa wasu jami’an soji da ake zargi da hannu a cikin shirin, ta hanyar bada tallafin kudi da wasu bayanai da suka shafi tsaron kasa.

A cewar rahoton, akalla jami’an soji 16 ne ke fuskantar bincike ciki har da Brigediya Janar, Kyaftin da Kolonel, bayan da Hedikwatar Tsaron Kasa ta tabbatar da cewa an kama wasu daga cikinsu bisa zargin aikata abubuwan da ba su dace ba.

Rahotanni sun ce ana gudanar da binciken ne ta hadin gwiwar Defence Intelligence Agency (DIA) tare da hukumomin tsaro na sauran bangarorin rundunar soja.

Duk da haka, Hedikwatar Tsaron (DHQ) ta bayyana cewa rahotannin da ke cewa an gano wani shirin juyin mulki ba gaskiya ba ne, tana mai cewa wannan labarin;
“ƙarya ce da aka kirkira domin tada hankalin jama’a.”

DHQ ta kara da cewa binciken da ake yi yana cikin tsarin doka kuma gwamnati ba za ta lamunci duk wani yunkuri da zai kawo barazana ga zaman lafiya da tsarin dimokuraɗiyya a ƙasar ba.

Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.


(Dailytrust)

Post a Comment

0 Comments