Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da cewa darussan Turanci da Lissafi za su ci gaba da kasancewa lallai ne ɗalibai su yi su a jarrabawar O-Level, kuma su samu nasara a kan su (Credit).
Ma’aikatar Ilimi ta bayyana hakan ne domin gyara rudanin da ya bazu a kafafen sada zumunta, inda wasu rahotanni suka yi ikirarin cewa gwamnati ta soke darussan.
A cikin wata sanarwa da Daraktar Yaɗa Labarai ta Ma’aikatar, Folasade Boriowo, ta fitar, an jaddada cewa babu wani sabon tsarin da ya soke wajibcin waɗannan darussa, sai dai gwamnati na sake nazarin wasu sharuɗɗan shiga jami’a ne kawai.
Ministan Ilimi, Dr. Maruf Tunji Alausa, ya ce:
“Turanci da Lissafi su ne ginshiƙan ilimi. Babu wani sabon tsari da zai cire su daga cikin darussan da dole ne ɗalibai su rubuta.”
Ya kuma ja hankalin ɗalibai da iyaye da su daina yarda da jita-jita ko labaran ƙarya da ke yawo a yanar gizo, su dogara da bayanan hukumomin gwamnati kawai.
“Manufar gwamnati ita ce samar da tsarin da zai baiwa ɗalibai damar samun ingantaccen ilimi, ba rage ƙimarsa ba,” in ji Ministan.
Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.
0 Comments