Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International ta nuna damuwa kan kama ɗan jarida Ibrahim Dan’uwa Rano da jami’an ’yan sanda suka yi a jihar Kano, inda ta bayyana cewa matakin ya sabawa ’yancin faɗar albarkacin baki da tsarin mulkin ƙasa ya tanada.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, ƙungiyar ta bayyana cewa kama Dan’uwa Rano saboda aikin jarida da yake yi ba bisa ƙa’ida ba ne, kuma yana nuna yadda ake amfani da jami’an tsaro don cusgunawa kafafen yaɗa labarai masu zaman kansu.
Amnesty International ta ce zargin da rundunar ’yan sanda ta yi cewa ɗan jaridar na gudanar da gidan talabijin na intanet ba tare da lasisin Hukumar NBC ba, babu hujja ko doka da ke baiwa NBC iko akan irin waɗannan kafafe na intanet.
Ƙungiyar ta yi kira ga hukumomin tsaro da su saki Ibrahim Dan’uwa Rano ba tare da wani sharadi ba, tare da janye duk wani mataki da ke nuna ƙoƙarin hana ’yancin aikin jarida da faɗar albarkacin baki a ƙasar.
Amnesty International ta kuma ja hankalin hukumomin Najeriya da su girmama dokokin ƙasa da ƙasa da suka tanadi kariya ga ’yan jarida da masu aikin yaɗa labarai.
Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.
0 Comments