Jam’iyyar APC ta jihar Zamfara ta karyata jita-jitar da ke yawo cewa ta kafa wani kwamiti domin karɓar Gwamna Dauda Lawal daga PDP zuwa APC.(Dauda lawal)
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar a jihar ya fitar, jam’iyyar ta bayyana cewa labarin da ake yadawa ba shi da tushe ballantana majama kuma ƙarya ce tsagwaron ta siyasa da wasu ke amfani da ita don tada hankalin jama’a.
Sanarwar ta ce jam’iyyar APC ba ta kafa wani kwamiti ba, kuma babu wani shiri na musamman da ya shafi karɓar wani daga jam’iyyar PDP a halin yanzu.
APC ta jaddada cewa tana mai da hankali kan ƙarfafa gininta a Zamfara, tare da ci gaba da goyon bayan shugabancin jam’iyyar a matakin ƙasa.
Ta kuma shawarci jama’a da su guji yarda da ƙaryar siyasa da ake yadawa a kafafen sada zumunta, tare da tabbatar da cewa duk wani rahoto daga jam’iyyar zai fito ta hanyoyin yada labaran APC.
Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.
0 Comments