An Zargi Wasu Jami'an Soji Da Yunkurin Juyin Mulki a Najeriya

Rundunar sojin Najeriya ta kafa wani kwamiti na musamman domin binciken wasu jami’ai 20 da ake zargin su da hannu a yunkurin juyin mulki da nufin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Majiyar soji ta bayyana wa jaridar Premium Times cewa lamarin ya faru ne a ƙarshen watan Satumba, inda ake zargin jami’an da shirya zubar da jini da kuma kashe manyan jami’an gwamnati idan har shirin nasu ya yi nasara.

Rahotanni sun nuna cewa cikin waɗanda ake zargin an tsara yi wa kisan gilla akwai Shugaba Tinubu, mataimakin sa Kashim Shettima, da kuma shugabannin majalisun tarayya, Sanata Godswill Akpabio da Abbas Tajudeen, tare da wasu fitattun jami’an gwamnati.

Majiyar ta ce waɗanda ake zargin sun tsayar da takamaiman ranar aiwatar da juyin mulkin, tare da ci gaba da tuntuɓar juna kafin jami’an tsaro su gano shirin.

Rahoton ya kuma bayyana cewa bayan an gano wannan makirci, lamarin ya tayar da hankula a fadar gwamnati, duk da cewa babban hafsan sojin ƙasa ya tabbatar wa gwamnatin Najeriya da cewa rundunar soji tana nan cikin cikakken biyayya da goyon baya ga tsarin mulkin demokuraɗiyya.

Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.

(Premier Radio kano)

Post a Comment

0 Comments