Rundunar sojin Najeriya ta sanar da cewa dakarunta sun samu gagarumar nasara bayan sun ceto mutum 23 da suka haɗa da ’yan ƙasar China huɗu daga hannun masu garkuwa da mutane a yankin Chigogo Hills, jihar Kwara.
A cikin sanarwar da rundunar ta fitar, an ce an gudanar da irin wannan aikin a sassan ƙasar daban-daban, inda aka kama manyan masu tallafa wa ’yan ta’adda da kayan da suke amfani da su wajen sadarwa da samun bayanai.
A jihar Borno, sojojin Operation HADIN KAI sun cafke wasu ’yan ƙasar Chadi guda uku a garin Ngala, bayan an same su da na’urorin Starlink guda 12 da kuma batirin hasken rana da ake zargin suna kaiwa ga ’yan Boko Haram da ISWAP.
Haka nan a Yobe, jami’an tsaro sun dakile wani yunkuri na kai kayan abinci da mai ga ’yan ta’adda, yayin da suka kama wani mai tukin keke Napep da ke ɗauke da man fetur.
A Kogi State, dakarun haɗin gwiwa na Operation MESA sun cafke mutane hudu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a kauyen Akuna.
A Imo State, rundunar Operation UDO KA ta kai samame wani otal da ake zargin mafakar masu garkuwa da mutane ce a Ngor Okpala, inda aka kama mutane shida ciki har da wasu da suka sanya kayan ’yan sanda da kuma ma’aikatan otal ɗin.
A yankin Niger Delta, jami’an Operation Delta Safe sun lalata wuraren tace danyen mai da ake sarrafawa ba bisa ƙa’ida ba, inda aka kwace man dizal lita 775 da man gyara lita 150 daga hannun masu fasa mai a jihohin Delta da Rivers.
Sojojin sun ce wadannan nasarorin na nuna yadda suke ƙara ƙaimi wajen murƙushe ’yan ta’adda, masu garkuwa da mutane, da masu lalata tattalin arzikin ƙasa.
Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.
0 Comments