Gwamnatin Jihar Jigawa ta kaddamar da shirin samar da sabbin tashoshin ruwan sha da ke amfani da hasken rana a wasu kananan hukumomin jihar, domin sauƙaƙa wa al’umma samun ruwa mai tsafta da dorewa.
Manajan Darakta na Hukumar Ruwa ta Jihar, Injiniya Zayyanu Rabi’u Kazaure, ya bayyana haka a Dutse, inda ya ce gwamnati ta amince da kashe Naira miliyan 400 don aikin.
A cewarsa, za a gina tashoshin ne a Hadejia, Ringim, Birnin Kudu, Kafin Hausa, da kuma sabon rukunin gidaje na Kazaure, domin tabbatar da cewa ko da al’umma a ƙauyuka suna samun ruwa mai tsafta cikin sauƙi.
Injiniya Zayyanu ya bayyana cewa samar da ruwan sha mai inganci na ɗaya daga cikin muhimman ajandar Gwamnatin Jihar Jigawa, tare da yabawa gwamnati bisa jajircewarta wajen ciyar da jama’a gaba da kare lafiyar su.
Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.
0 Comments