Gwamnatin Jihar Kano ta dauki sabon mataki na inganta harkokin lafiya, ta hanyar amincewa da shirin saka wutar hasken rana da kuma siyan sabbin kayan aikin lafiya a wasu muhimman asibitoci uku Fagwalawa Cottage Hospital, Ajingi General Hospital, da Doguwa General Hospital.
Hukumar kula da asibitocin jihar ta bayyana cewa aikin zai gudana ne karkashin Kano Health Trust Fund (KHETFUND) a jagorancin Dr. Fatima Zaharaddeen, domin tabbatar da dorewar wutar lantarki da ingantaccen aikin asibiti.
Shugaban hukumar, Dr. Mansur Mudi Nagoda, ya bayyana cewa wannan shiri na daga cikin nasarorin da ake samu a karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda ke da kwarin gwiwar gyara da sabunta tsarin kiwon lafiya a jihar.
A cewar Dr. Nagoda, shirin zai taimaka wajen tabbatar da cigaba da aikin likitoci ba tare da tangarda ba, musamman a wuraren da ake fuskantar matsalar wutar lantarki, yayin da sabbin kayan aikin za su taimaka wajen gano cututtuka da bayar da magani cikin inganci.
Haka kuma, Dr. Fatima Zaharaddeen ta jaddada cewa KHETFUND za ta tabbatar da an aiwatar da dukkan ayyukan bisa tsari, domin ganin an cimma manufar gwamnati ta samar da lafiya ga kowa da kowa.
Gwamnatin Kano karkashin Alhaji Abba Kabir Yusuf na ci gaba da nuna jajircewa wajen inganta bangaren lafiya ta hanyar zuba jari a cikin gine-gine, horar da ma’aikata, da kuma amfani da sabbin fasahohi, domin tabbatar da cewa duk dan Kano yana da damar samun kulawar lafiya mai inganci ko a birni ko karkara.
Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.
0 Comments