Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa ta raba tallafin Naira miliyan 31 ga iyalan jami’ai 59 da suka rasu yayin A lokacin dq suke bada tsaro ga Alumma, domin rage musu raɗaɗin rashin masoyan da suka sadaukar da rayuwarsu wajen kare ƙasa.
Mai magana da yawun rundunar, SP Lawan Shiisu Adam, ya ce wannan tallafi na daga cikin shirin na musamman da hukumar ta tanada domin kula da iyalan jami’an da suka mutu a bakin aiki.
A cewar Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Jigawa, CP Dahiru Muhammad, rundunar ta yi wannan taimako ne a matsayin girmamawa ga irin jajircewar da mamatan suka nuna wajen tabbatar da zaman lafiya da kare al’umma.
Ya kuma yi kira ga iyalan da su yi amfani da tallafin ta hanyar inganta makomar ’ya’yansu da kuma ci gaban rayuwar iyali baki ɗaya.
Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.
0 Comments