Ba dai dai ba ne Gwamnati ta cigaba da Ciyo bashi Bayan An Cire Tallafin Mai

Ba dai dai ba ne Gwamnati ta cigaba da Ciyo bashi Bayan An Cire Tallafin Mai.

(Sunusi)

Tsohon Gwamnan CBN, Muhammadu Sanusi II, ya soki ci gaba da Karbo bashin da gwamnatin tarayya ke yi bayan cire tallafin man fetur (subsidy), yana mai cewa Ina anfanin Cire tallafin to.

Sanusi ya ce cire Tallafin ya ƙara wa gwamnati samun kuɗaɗe, don haka bai kamata ta ci gaba da aron kuɗi ba.

Ya kuma kalubalanci yawan ministoci da kashe-ka-kashe da ya kira ɓarnar kuɗin gwamnati, yana mai cewa dole ne a daidaita kashe kuɗi.

Sanusi ya jaddada cewa dole a mayar da kuɗaɗen da aka samu daga cire subsidy zuwa inganta tattalin arziki, samar da ayyukan yi, da sauƙaƙa wa talakawa, idan ba haka ba, matakin zai zama a banza.

Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.

Post a Comment

0 Comments