Rundunar ‘yan sandan Babban Birnin Tarayya (FCT) ta kama mutum biyu da ake zargi da hannu a cikin kisan wata mata da suka yi amfani da dabara ta “one chance” wajen aikata laifin.
Kakakin rundunar, Josephine Adeh, ta tabbatar da kama mutanen, inda ta bayyana cewa an cafke su ne bayan cikakken bincike da aka gudanar a kan mutuwar wata mace da aka tsinci gawarta a gefen titi a unguwar Life Camp, Abuja.
An gano cewa mutanen suna cikin wata gungun masu amfani da mota wajen yaudarar fasinjoji, sannan su yi musu fashi da kuma cutarwa.
“Wadanda ake zargi sun amsa cewa suna amfani da mota wajen ɗaukar mutane a matsayin fasinjoji, daga nan sai su kai musu hari,” in ji kakakin rundunar.
Adeh ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike domin kama sauran membobin ƙungiyar da suka tsere, yayin da wadanda aka kama za a gurfanar da su gaban kotu da zarar an kammala binciken.
Ta kuma ja hankalin jama’a da su kasance cikin shiri, su guji hawa motocin da ba su da cikakkun bayanai ko takardu, musamman a lokacin dare.
Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.
0 Comments