Rundunar Yan sandan Jigawa Sun Kama Wani mutun Dauke Da Jabun Dalolin Amuruka

‘yan sandan jihar Jigawa sun kama wani mutum mai suna Lawan Isa, mai shekaru 33, bisa zargin mallakar takardun dalar Amuruka  na ƙarya guda 56 na dala $100.

Mai magana da yawun rundunar, SP Shi’isu Adam ne ya bayyana cewa an cafke wanda ake zargin a ranar 5 ga Oktoba 2025 da misalin ƙarfe 5 na yamma, a kasuwar Gidan Lage da ke ƙaramar hukumar Ringim.

A lokacin bincike, jami’an tsaro sun gano wayoyin Android guda huɗu da kuma wata waya mai maɓalli a hannun wanda ake zargi.

Sai dai rahotanni sun nuna cewa bai bayar da cikakken bayani ba kan yadda takardun kuɗin suka zo hannunsa.

A halin yanzu, an mika shi ga sashen binciken manyan laifuka (SCID) da ke Dutse domin zurfafa bincike.

SP Shi’isu ya bayyana cewa rundunar tana ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da tsaro da kuma dakile ayyukan masu aikata laifi a dukkanin sassan jihar.

Ya kuma shawarci jama’a da su kasance masu faɗakarwa tare da bayar da bayanai ga hukumomin tsaro idan suka lura da wani abin da bai dace ba.

“Ya zama dole mu haɗa kai domin ganin an kawar da ayyukan masu yaudara da masu kutse cikin tattalin arzikinmu.” — in ji SP Shi’isu Adam.

#Fitacciya #Jigawa #YanSanda #Laifi #Tsaro #nacce

Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.

Post a Comment

0 Comments