Jirgin Boeing 737-700 Business Jet na shugaban ƙasa, wanda gwamnatin Najeriya ta sanya a kasuwa watan Yulin 2025, har yanzu bai samu mai siya ba kusan watanni huɗu bayan an ɗora shi a shafin sayar da jiragen sama na ƙasashen waje.
Kamfanin da ke da Alhakin saida Jiragen ne ya tabbatarwa da Jaridar punch, ta hanyar musayar Sakkonnin Email tsakanin wakilin jaridar PUNCH da kamfanin da ke kula da tallan jirgin, JetHQ dake Amurka.
Marinell Nuevo, mai taimakawa Kamfanin dillancin jiragen na JetHQ, ne ya tabbatar cewa jirgin "har yanzu yana nan ba a sayarwa yake".
Sai dai Manajan da ke kula da harkokin kasuwa, Laurie Barringer, ta ki bada wasu bayanan inda tace masu mallakin jirgin kadai ke da hakkin samu.
An ce jirgin na ƙarƙashin kulawar AMAC Aerospace da ke Switzerland, kamfani da ya ƙwarewa a gyare-gyare da sayar da jirage.
Kamar yadda bayanan tallan suka nuna, an yi wasu gyara-gyara a cikin jirgin:
canza kujerun ajin farko (first-class seats), ƙara sabon ɗarɓar kwandunan ƙafa (cabin carpets), da kuma yin manyan bincike (inspections) na C1–C2 a Basel a watan Yuli 2024.
Jirgin na ɗauke da kujeru 33 ga fasinjoji, tare da ma’aikata (crew) 8, jimlar kujeru 41.
Bugu da ƙari, kimar matsakaicin jirgin Boeing BBJ da shafin aircraftcostcalculator.com, ya bayar ya kai kimanin dalar Amuruka miliyan hamsun da Shida ($56 million US Dollars) idan aka yi la'akari da yadda aka gyara shi da kuma yanayin yadda ake kula da shi.
0 Comments