Gwamnan Katsina ya musanta battun tattaunawa da ‘yan ta’adda,domin ya ƙarfafa tsaro ga a al’umma
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, ya musanta jita-jitar da ke cewa gwamnatin sa tana tattaunawa da ‘yan ta’adda.
Ya bayyana cewa gwamnati ba za ta taɓa tattaunawa da ‘yan ta’adda ba, sai dai tana ƙoƙarin samar da zaman lafiya ta hanyoyin da suka dace.
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin ƙaddamar da sabbin jami’an Community Watch Corps (C-Watch) guda ɗari, da za su fara aiki a ƙananan hukumomi 20 a fadin jihar.
Ya ce:
“Labaran Jaridu sun ce Gwamnatin Jihar Katsina tana tattaunawa da ‘yan ta’adda, amma hakan ba gaskiya bane.
Gwamnati ba za ta tattauna da su ba, amma za ta yi maraba da zaman lafiya idan sun tuba.”
Radda ya ce gwamnatin sa ta ƙirƙiri Katsina Model, wadda ta mayar da hankali kan haɗin gwiwar al’umma wajen kawo ƙarshen ta’addanci.
A cewarsa, al’ummomin da abin ya shafa su ne ke fara tattaunawa da waɗanda suka tuba, sannan gwamnati ta ba su tallafi da kariya.
Ya kuma bayyana cewa wasu yankuna kamar Jibia, Batsari, Danmusa, Safana, Faskari, da Sabuwa sun samu watanni da dama na kwanciyar hankali saboda wannan tsarin.
Haka kuma, gwamnan ya ce an horar da jami’an C-Watch a fannonin dabaru, sadarwa, da kare hakkin bil’adama, tare da neman su kasance masu ƙwarin gwiwa da gaskiya wajen aikin su.
“Ba za mu taɓa sakar wa ‘yan ta’adda fuska ba, amma za mu yi maraba da duk wanda ya dawo da Makaman sa” in ji Radda.
Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.
0 Comments