Mutane goma sha ɗaya (11) ne suka rasa rayukansu a wani mummunan harin ’yan bindiga A Plateau

Mutane goma sha ɗaya (11) ne suka rasa rayukansu a wani mummunan harin ’yan bindiga a ƙauyukan Rachas (Heipang) da Rawuru (Fan), ƙaramar hukumar Barkin Ladi, a jihar Plateau, sun samu jana’izar hadin gwiwa a yau Laraba.

Rahotanni sun bayyana cewa, harin da aka kai a daren Talata ya ritsa da mazauna yankin, inda wasu ’yan bindiga suka bude wuta ba tare da kakkautawa ba, lamarin da ya janyo asarar rayuka da dama ciki har da mata da kananan yara.

An gudanar da jana’izar a cikin yanayi na bakin ciki da kuka daga iyalai, abokai da makwabta.

Daga cikin waɗanda suka rasu akwai:

Chollom Danjuma (37)
Sunday Gyang (27)
Kefas Dung (28)
Solomon Dung (40)
Mrs. Christy Dung (3)
Marvellous Pam (9)
Davou Manam (25)
Japheth Solomon (7)
Mancha Monday (7)
Nyam Chollom (5)
Maryann Mancha (10)

Ƙungiyar matasa ta Berom Youth Moulders (BYM) ta bayyana cewa al’ummar Barkin Ladi da Riyom sun gaji da irin wadannan hare-hare da ke ci gaba da faruwa ba tare da kawo karshen su ba.

A wata sanarwa da ta fitar, ƙungiyar ta yi kira ga gwamnati da jami’an tsaro su tashi tsaye wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a, tare da tabbatar da cewa duk wanda ke da hannu cikin kisan ya fuskanci hukunci mai tsanani.

Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa;

“Rayuwa ta zama kamar babu tsaro a yankinmu.Yanzu mutane na tsoron zuwa gonaki saboda tsoron harin gilla.”

Hukumomin tsaro dai sun tabbatar da cewa suna ci gaba da bincike don gano wadanda ke da alhakin kai wannan hari.

💬“Abin bakin ciki ne yadda mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba suke rasa rayukansu a cikin gidajensu.”

Post a Comment

0 Comments