An sace wa Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na Jihar Kaduna, Barista Sule Shu’aibu (SAN), wayar hannunsa a bainar jama’a

Rahotanni sun bayyana cewa an sace wa Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na Jihar Kaduna, Barista Sule Shu’aibu (SAN), wayar hannunsa a bainar jama’a yayin wani muhimmin taro da aka shirya kan batutuwan tsaro a jihar.

Lamarin dai ya faru ne a ranar Alhamis, lokacin da kwamishinan ya halarci taron da aka shirya domin tattauna hanyoyin magance matsalolin tsaro da ke addabar jihar Kaduna da kewaye.

Shaidun da abin ya faru a gaban sun ce an gano satar wayar ne bayan an kammala taron, abin da ya jawo tambayoyi masu yawa kan yadda mai laifi ya samu damar aikata irin wannan abu a wurin da ke cike da jami’an tsaro.

Wata majiyar da ke kusa da ofishin ma’aikatar ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa an dauki matakan bincike domin gano wanda ke da hannu cikin satar.

Sai dai har zuwa lokacin da ake haɗa wannan rahoto, ba a kama wanda ake zargi ba, kuma hukumar tsaro ko gwamnatin jihar Kaduna ba su fitar da wata sanarwa ta hukuma kan batun ba.

Lamarin ya tayar da cece-kuce a kafafen sada zumunta, inda jama’a ke tambaya kan yadda jami’an tsaro ke gudanar da aikin su idan har kwamishina zai rasa wayarsa a taron da ya shafi tsaro.

Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.

Post a Comment

0 Comments