By Bello Galladanci (Dan Bello)
Dan BelloGaskiya ta fara fitowa akan batun kisan kare dangi a Najeriya. Sabbin takardu daga ma’aikatar shari’ar amurka sun fallasa wani abu mai matuƙar hatsari.
Fitacciya ta rawaito cewa, wasu kungiyoyin neman biyafara a ƙasashen waje ne suka kaddamar da yaƙin zargin cewa ana “kisan gilla ga kiristoci a Najeriya.” Kamar yadda jaridar Guardian ta buga. Wannan ya sa donald trump da sanata ted cruz suka bayyana Najeriya a matsayin ƙasa mai “takatsantsan kan ’yancin addini.” Sanata cruz ya ce, “babu ƙasa a duniya da ake zaluntar kiristoci kamar Najeriya.” Ya kawo boko haram da ’yan ta’adda, eh, mun san su da laifinsu, amma ga hakikanin magana.
Wannan zargi na kisan kare-dangi ana shiryawa, ana ɗaurawa, ana turawa ƙasashen waje ne daga hannun waɗannan ’yan biyafara da ke zaune a ƙasashen waje. Takardun DOJ suna da danganta da kamfen ɗin ƙungiyar United States of Biafra, ciki har da gwamnatin biyafara da suke cewa tana “cikin hijira.” Sun ɗauki masu lobin siyasa a Washington, sun rattaba hannu a kan wasu takardu a Finland, suna ƙoƙarin nuna Najeriya a matsayin ƙasa mai kisan kiyashi, ba don magance matsalolin gida ba, sai don neman karɓuwa a amurka. Ɗaya daga cikin manyansu, Simon Ekpa, yanzu haka yana gidan yari a Finland saboda laifukan ta’addanci, zambar haraji, da tada fitina. Amma kuma shi ake sanyawa hannu a takardun da ke zargin Najeriya da kisan kare-dangi.
Takardun sun nuna wani abu mafi muni. Saƙonninsu ana yi ne musamman domin jan hankalin wasu ’yan siyasar amurka, musamman magoya bayan trump, da zancen cewa goyon bayan biyafara zai “ceto kiristoci” kuma zai takaita tasirin china. Ku saurara da kyau. Wannan ba wayar da kai ba ce. Wannan inji ne na siyasa da ake sarrafa shi daga ƙasashen waje. An tsara shi. Ana ɗaukar nauyinsa. An tura shi ne don canza yadda turawan waje ke kallon Najeriya. Waɗannan kamfen-kamfen da ake haɗawa da kalmomin “kisan kare-dangi” da “zaluncin addini” na iya kunna fitinar kabilanci a cikin gida, su kuma ɓata sunanmu a idon duniya.
0 Comments