Wasu manyan ’yan majalisa masu ci da tsofaffi daga majalisar dokokin jihar kano sun bayyana goyon bayansu ga barau jibrin, mataimakin shugaban majalisar dattawa, domin ya tsaya takarar gwamna a zaben 2027.
Fitacciya ta rawaito cewa, kusan wakilai 200 ne suka ziyarci barau a karkashin jagorancin tsohon shugaban majalisar jihar, Abdulaziz G. Gafasa, inda suka bayyana shi a matsayin ɗan takarar da ya dace a jam’iyyar APC saboda ayyukansa a majalisar tarayya da gudunmawarsa ga yankuna daban-daban na jihar.
Wakilan sun jaddada cewa za su yi amfani da tasirin da suke da shi a tsakanin al’umma domin tallata barau a dukkan matakai.
A nasa bangaren, barau ya bayyana farin cikinsa kan wannan goyon baya tare da kiransu su ci gaba da hada kai don maido da martabar kano.
Ya kuma ce bai yanke shawarar ayyana takara ba tukuna, sai dai ya tabbatar masu da cewa zai ci gaba da aiki tare da su wajen ganin cigaban jihar ya tabbata.
0 Comments