Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya mika motocin sintiri da aka kera a Najeriya ga hukumomin tsaro

Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya mika motocin sintiri da aka kera a Najeriya ga hukumomin tsaro domin ƙara ƙarfin yaki da rashin tsaro.

Fitacciya ta rawaito cewa, bikin ya gudana a Gidan Gwamnati, Yola, inda Mataimakin Gwamna, manyan jami’ai, da shugabannin tsaro suka halarta.

Gwamna Fintiri ya yaba wa hukumomin saboda sanya Adamawa cikin jihohin Najeriya mafi zaman lafiya, ya kuma ce motocin za su taimaka wajen tabbatar da tsaro da ƙarfafa ma’aikatan gaba ɗaya.
Shugabannin tsaro, karkashin jagorancin Brigadier Janar Ogbonnaya Amechi Agwu, sun gode wa Gwamna, suna mai cewa motocin za su inganta saurin amsa lamuran tsaro da kuma magance matsalolin tsaro na cikin gida.

Post a Comment

0 Comments