![]() | |
| Minister of Information, Mohammed Idris |
Gwamnatin Tarayya ta roƙi jama’a da su haɗa kai wajen yaki da matsalar rashin tsaro a ƙasa nan, tare da bayar da gudummawa domin ganin an samu nasara.
Fitacciya ta rawaito cewa, gwamnatin ta jaddada cewa haɗin kan al’umma shi ne mabuɗin magance ta’addanci, satar mutane da sauran barazanar tsaro, kuma tana kira ga jama’a da su tabbatar da sahihancin bayanai kafin su yada domin gujewa tada tarzoma ko rikice rikice.
Haka kuma, gwamnati ta bayyana cewa yaki da rashin tsaro ba aikin jami’an tsaro kaɗai ba ne, har ila yau ya rataya a wuyan kowa.
sojoji da sauran hukumomin tsaro na buƙatar tallafin bayanai daga al’umma domin gano maboyar ‘yan ta’adda da mayar da martani cikin sauri.
Gwamnatin ta ƙara da cewa samar da ingantattun hanyoyin sadarwa da tsarin bayar da rahoto ga hukumomin tsaro zai taimaka wajen tabbatar da tsaro mai dorewa da zaman lafiya a ƙasa.
punch

0 Comments