Muhimmancin Shan Ruwa Ga Lafiya
Ruwa shi ne ginshiƙin rayuwa. Kashi mafi girma na jikin ɗan Adam ruwa ne, kuma babu abin da jiki zai iya yin aiki yadda ya kamata ba tare da ruwa ba. Duk da haka, mutane da dama ba sa bai wa shan ruwa muhimmanci kamar yadda ya dace.
1. Ruwa yana taimaka wa jiki wajen daidaita zafi
Lokacin da jiki ya fara yin zafi, musamman yayin zafi ko motsa jiki, jiki yana fitar da gumi domin sanyaya kansa. Idan mutum bai sha ruwa ba sosai, wannan tsarin zai lalace, wanda zai iya jawo gajiya ko suma saboda rashin ruwa (dehydration).
2. Yana taimakawa wajen narkar da abinci
Ruwa yana taimakawa wajen narkar da abinci a ciki, yana sauƙaƙa motsin abinci a hanji, kuma yana hana mutum fama da maƙoshin ciki ko maƙarƙashiya. Shan ruwa kafin da bayan cin abinci yana taimaka wa tsarin narkewa sosai.
3. Ruwa yana taimaka wa ƙoda (kidneys)
Ƙoda na amfani da ruwa wajen tace datti da sinadarai marasa amfani daga jini. Idan jiki bai samu isasshen ruwa ba, datti na iya taruwa, wanda zai iya jawo matsalar ƙoda ko duwatsun ƙoda (kidney stones).
4. Yana ƙara kuzari da lafiyar fata
Mutanen da ke shan ruwa sosai sukan sami fata mai laushi da haske. Rashin ruwa a jiki yana sa fata bushewa da tsufa da wuri. Haka kuma, ruwa yana taimakawa wajen kawar da gajiya da kasala.
5. Ruwa yana taimaka wa kwakwalwa da hankali
Kashi mai yawa na kwakwalwar ɗan Adam ruwa ne. Idan jiki ya rasa ruwa, mutum na iya fuskantar rashin natsuwa, ciwon kai, da sauyin yanayi. Shan ruwa akai-akai yana taimaka wa kwakwalwa yin aiki cikin natsuwa da sauri.
6. Ruwa yana taimaka wajen rage kiba
Shan ruwa kafin cin abinci yana sa mutum jin cika da wuri, wanda ke taimakawa wajen rage yawan abincin da ake ci. Haka kuma, ruwa baya ƙara kalori, don haka yana da kyau a maye gurbin abin sha mai sukari da ruwa.
Yadda Ake Shan Ruwa Ta Hanya da zai anfanar Amfanar da kai
A fara rana da gilashin ruwa ɗaya kafin cin komai.
A ci gaba da shan ruwa kadan-kadan a rana.
Kada a jira a ji ƙishirwa kafin a sha ruwa.
A guji shan ruwa da yawa lokaci guda bayan cin abinci sosai.
Shan ruwa yana da sauƙi, amma amfaninsa ba shi da iyaka. Ka mai da shi al’ada a rayuwarka domin samun lafiya, kuzari da natsuwa a jiki da hankali.
Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.
0 Comments