Babban hafsan sojojin Najeriya, laftanar janar waidi shaibu, ya bayyana shirin daukar sabbin sojoji 24,000 domin karfafa rundunar sojin kasar a yaki da matsalolin tsaro.
Fitacciya ta rawaito cewa, janar shaibu ya sanar da hakan a kaduna yayin ziyarar aiki da ya kai runduna ta 1 inda ya ce sabbin cibiyoyin horaswa guda uku da shugaban kasa bola tinubu ya amince da su za su samar da sojojin da suka kware a sabon dabarun yaki da horo na zamani.
Ya ce rundunar na fatan horas da sojoji 12,000 cikin watanni shida kuma idan an gudanar da horaswa a matakai biyu za a iya samar da jimillar dakarun 24,000.
Babban hafsan ya jaddada cewa shirin ba wai kara yawan sojoji ba ne kawai har ma da tabbatar da inganci da kwarewa da kuma shirin tunkarar barazanar tsaro da ke kara kamari a fadin kasar nan.
Ya kuma tabbatar da kudirin rundunar na inganta jin dadin ma’aikata a karkashin manufar soja na farko.
Ana sa ran sabbin dakarun za su karfafa martanin sojoji su kare al’umma kuma su inganta tsaro a manyan yankunan da ake fama da rikice-rikice.
0 Comments