Dakarun rundunar Operation Hadin Kai sun yi nasarar dakile wani harin ba zata da mayakan Boko Haram da ISWAP sama da 300 suka kai musu a jihar Borno.
Fitacciya Ta rawaito cewa, lamarin ya faru ne da misalin karfe 2:50 na daren ranar Asabar a garin Chibok da ke a Ƙaramar Hukumar Chibok ta jihar Borno.
Bayanai sun nuna cewa 'yan ta'addan sun yi yunkurin shiga garin ta bangarori daban daban, amma dakarun 28 Task Force Brigade sun yi amfani da na'urorin hangen nesa wajen gano su tun kafin su karaso.
An shafe sama da sa'o'i biyu ana musayar wuta mai zafi tsakanin bangarorin biyu, wanda hakan ya tilasta wa 'yan ta'addan tserewa zuwa yankin Timbuktu Triangle bayan sun sha kashi.
Rahotanni sun tabbatar da cewa babu wani soja da ya rasa ransa ko ya jikkata a harin, sannan jiragen yakin Sojin Saman Najeriya NAF sun bi sahun 'yan ta'addan da ke gudu tare da kai musu hare hare.
0 Comments