Duk da umarnin da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bayar na janye jami'an 'yan sanda daga aikin tsaron manyan mutane (VIPs), har yanzu akwai jami'an 'yan sanda na kwantar da tarzoma (MOPOL) da ke ci gaba da aikin gadi a kamfanoni masu zaman kansu da sauran cibiyoyi.
Fitacciya Ta rawaito cewa, binciken da jaridar Punch ta gudanar ya nuna cewa jami'an 'yan sandan da ke aiki a kamfanoni daban-daban a Abuja na nan daram a bakin aikinsu.
Shugaban Ƙasa Tinubu ya bayar da umarnin janye jami'an 'yan sandan ne daga aikin tsaron VIPs domin a tura su zuwa manyan ayyukan 'yan sanda na tabbatar da tsaro.
A ranar Alhamis, Sufeto Janar na 'Yan Sanda, Kayode Egbetokun, ya bayyana cewa an riga an janye jami'ai 11,566 daga wurin VIPs.
Sai dai bincike a kamfanoni da dama a Abuja ya nuna cewa jami'an suna nan suna ci gaba da aikinsu, inda wani jami'in dan sanda da ke gadi a wani kamfanin gine-gine ya ce ba a ce musu su tafi ba.
Haka zalika, wani ma'aikacin kamfani a yankin Jabi na Abuja ya tabbatar da cewa 'yan sandan da ke gadin ofishinsu suna nan suna zuwa aiki, inda ya ce umarnin bai shafi wadanda ke aiki a kamfanoni ba.
Mai Magana da Yawun Rundunar 'Yan Sanda, Benjamin Hundeyin, bai samu damar tabbatar da ko an cire kamfanoni daga cikin wannan umarni ba.
0 Comments