Ambaliya ta lalata gidaje da gonaki a Neja


Ambaliyar ruwa ta lalata gidaje, wuraren kiwon kifi da kuma manyan gonaki a garin Muye da wasu unguwannin da ke kusa da shi a Ƙaramar Hukumar Lapai ta Jihar Neja.

Fitacciya ta rawaito cewa, ambaliyar ta faru ne bayan Kogin Gurara ya cika sakamakon mamakon ruwan sama da aka samu a wannan daminar.

Etsu Muye, Alhaji Salihu Muhammadu, ya bayyana cewa ambaliyar ta kuma mamaye kasuwanni tare da katse hanyoyin da suka haɗa al’ummomin yankin.

Ya ce gonaki da wuraren kiwon kifi da dama, waɗanda al’ummar yankin ke dogaro da su wajen samun abinci da kuɗin shiga, sun lalace bayan ruwan ya cika su da yashi.

Salihu Muhammadu ya kuma nuna damuwa kan tafiyar hawainiyar aikin gina katangar kariya daga ambaliyar ruwa da Hukumar Bunƙasa Yankunan da Ke Samar da Wutar Lantarki ta Ruwa (N-HYPPADEC) ke gudanarwa a kan kuɗi Naira miliyan 700.

Ya yi kira ga gwamnati da ɗan kwangilar aikin da su gaggauta kammala katangar domin kare al’ummomin yankin daga ƙarin ɓarnar da ambaliyar ruwa ka iya haifarwa.

Me za ku ce?

©Aminiya

Post a Comment

0 Comments