Fagge ya nemi Ministan Shari'a ya shiga tsakani kan tsare Maryam Shehu



Lauyan kare hakkin ɗan Adam, Abba Hikima Fagge, ya yi kira ga Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya da ya shiga tsakani kan tsare Maryam Isah Shehu, wadda ya ce Hukumar EFCC ta shafe kwanaki 35 tana tsare da ita kafin daga bisani ta shigar da ƙara mai zargi ɗaya a kanta.

Fagge ya bayyana cewa, Maryam, ɗalibar shekarar ƙarshe a Jami’ar Bayero Kano (BUK), ta shafe kwanaki 35 a hannun EFCC, duk da cewa hukumar ta sha ƙin ba ta beli. Ya ce hukumar ta garzaya kotu ne da ƙarar da ta shafi wani rubutu da Maryam ta wallafa a kafafen sada zumunta.

A cewarsa, abin da Maryam ta yi shi ne bayyana zargin cin hanci da rashawa da ya shafi wani Daraktan Yanki na EFCC, amma har yanzu hukumar ba ta bayyana wa ’yan Nijeriya ko ta gudanar da bincike mai zaman kansa kan zargin ba, ko kuma sakamakon binciken da aka yi.

Fagge ya ce abin damuwa shi ne, a maimakon bincikar zargin da aka yi, an kama tare da tsare wadda ta bayyana zargin, yayin da a cewarsa, ainihin zargin ya kasance ba tare da wani bincike na gaskiya da bayyane ba.

Ya ƙara da cewa, a cikin ƙarar, EFCC na zargin Maryam da niyyar ɓata sunan hukumar, amma ya tambayi ko me zai fi ɓata sunan hukumar fiye da tsare ɗan ƙasa na tsawon kwanaki 35, ƙin ba shi beli, sannan a shigar da ƙara mai zargi ɗaya bayan wannan lokaci.

Fagge ya kuma ce an miƙa wa Maryam takardar ƙarar ne a jajibirin ranar da za a gurfanar da ita a gaban kotu, lamarin da ya ce ya hana lauyoyinta samun isasshen lokaci na shirya kare ta da kuma gabatar da bukatar beli yadda ya kamata.

Ya yi kira ga Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya da ya gaggauta duba lamarin, yana mai cewa yadda EFCC ta gudanar da shari’ar na iya haifar da tambayoyi kan amfani da iko ba bisa ka’ida ba, tare da jefa Najeriya cikin suka a idon ƙasashen duniya.

Fagge ya jaddada cewa doka ya kamata ta kare wanda ya kawo zargi kamar yadda take binciken zargin, yana mai kira da a ba Maryam beli tare da gudanar da bincike mai zaman kansa da gaskiya kan zargin da aka yi wa jami’in EFCC.

Me Za ku ce?

Post a Comment

0 Comments