'Yan sanda sun tarwatsa maboyar ’yan bindiga, sun ceto mutane uku da aka sace a Kaduna


Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta ce jami’anta tare da ’yan sa-kai sun tarwatsa maboyar wasu ’yan bindiga tare da ceto mutane uku da aka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Makarfi.

Fitacciya ta rawaito cewa lamarin ya faru ne a ranar 21 ga Agusta 2026, bayan rundunar ta samu sahihin bayanin sirri kan wasu mutane da ake zargin ’yan bindiga ne da ke gudanar da harkokinsu a yankin Gidan Mijin Gwaggo, Durum.

Jami’an ’yan sanda da ’yan sa-kai sun kai samame inda ’yan bindigar suka buɗe musu wuta, lamarin da ya haifar da musayar harbe-harbe. Daga bisani, ’yan bindigar suka tsere zuwa cikin daji dauke da raunukan harbin bindiga.

A yayin binciken wani gida mallakar Yakubu Sule, jami’an sun gano cewa ana amfani da gidan a matsayin maboyar ’yan bindiga, inda aka gano mutane uku da aka yi garkuwa da su, ciki har da Alhaji Hamza Shuaibu Gimi da wasu mutum biyu.

Rundunar ta ce an ceto mutanen ba tare da sun ji rauni ba, sannan aka kwato babur kirar Boxer da ake zargin masu garkuwar sun yi amfani da shi. An kuma mayar da waɗanda aka ceto ga iyalansu.

Kwamishinan ’Yan Sandan Kaduna, Rabiu Muhammad, ya yaba wa jami’an da ’yan sa-kan da suka gudanar da aikin, tare da tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da amfani da bayanan sirri da haɗin gwiwar al’umma wajen yaƙi da masu aikata laifuka.

Rundunar ta kuma yi kira ga jama’a da su kasance masu taka-tsantsan tare da ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai domin kare rayuka da dukiyoyi da kuma tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Me Za ku ce?

Post a Comment

0 Comments