Atiku ya yi alkawarin dawo da tallafin man fetur idan ya ci zaɓe

Atiku ya yi alkawarin dawo da tallafin man fetur idan ya ci zaɓe
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Atiku Abubakar, ya yi alkawarin dawo da tallafin man fetur idan aka zaɓe shi a matsayin Shugaban Ƙasar Najeriya a 2027.

Atiku ya bayyana hakan ne yayin da yake bayyana manufofinsa da shirinsa na tafiyar da ƙasar idan ya samu nasarar lashe zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa. 

Ya ce dawo da tallafin man fetur na daga cikin matakan da zai ɗauka domin rage wa ’yan Najeriya radadin tsadar rayuwa da kuma sauƙaƙa farashin makamashi.

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar ya kuma bayyana buƙatar ɗaukar matakan da za su inganta tattalin arziki tare da rage matsin da cire tallafin man fetur ya jefa al’umma ciki.

Alƙawarin na Atiku na zuwa ne a daidai lokacin da batun farashin man fetur da tasirin cire tallafin ke ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin manyan batutuwan da ake tafka muhawara a kai gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Post a Comment

0 Comments