Ministan Tsaro na Najeriya, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, ya yi murabus daga mukamin sa, inda ya bayyana dalilan rashin lafiya a matsayin hujjar daukar wannan mataki.
Fitacciya ta rawaito cewa, Badaru ya mika takardar ajiye aikin nasa ne ga Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu a cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan 1 ga Disamba, 2025.
Mai ba Shugaban Kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, shi ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa a ranar Litinin, inda ya ce Shugaba Tinubu ya karbi murabus din tare da gode wa tsohon ministan bisa hidimar da ya yi wa kasa.
Sanarwar ta kara da cewa ana sa ran Shugaban Kasa zai aikawa Majalisar Dattawa sunan wanda zai maye gurbin sa nan da karshen wannan mako.
Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Tinubu ke shirin kaddamar da dokar ta baci kan harkokin tsaro a fadin kasar, lamarin da ake ganin yana da nasaba da sake fasalin tsarin tsaron kasar.
0 Comments