Rundunar sojin Najeriya ta samu nasarar ragargazar gungun masu laifi a wani farmaki da ta kai a fadin kasar tsakanin ranar 29 ga watan Nuwamba zuwa 1 ga watan Disamba 2025.
Fitacciya Ta rawaito cewa, a yayin ayyukan rundunar ta halaka 'yan ta'adda takwas sannan ta kama wadanda ake zargi su 51 tare da ceto mutum 27 da kuma kwato makamai masu yawa.
A yankin Arewa maso Gabas dakarun runduna ta 151 da 152 da kuma 192 a jihar Borno sun halaka mayakan ISWAP da JAS guda hudu yayin farmaki da kwanton bauna. Sojojin sun kwato bindigogi kirar AK47 guda uku da harsasai iri daban daban da dama da rediyon sadarwa na Baofeng sannan sun dakile yunkurin shiga garin Chibok.
A jihohin Filato da Taraba da Benue da Kogi da Kaduna dakarun Operation WHIRL STROKE da Operation ENDURING PEACE sun ceto mutane a garuruwan Panyam da Zaki Biam da Tsanyawa da Kankia da Yagba West da Odo Eri da Karamar Hukumar Sanga da kuma Isoko North a jihar Delta.
Haka zalika an kama masu garkuwa da mutane biyu a Panyam da masu safarar mutane hudu a Sardauna da masu taimaka wa 'yan ta'adda uku a Ukum da masu hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba 13 a Lau da kuma dillalin bindigogi daya a jihar Filato mai suna Shuaibu Isah wanda aka fi sani da Alhaji.
A jihar Taraba sojoji sun halaka 'yan ta'adda hudu yayin rikicin kabilanci a Karim Lamido inda suka kwato bindigar AK47 ta gida daya da bindigogin toka uku da harsasai 25 da babura biyu. A jihar Filato kuma an kwato shanu 76 da aka sata.
A yankin Kudu maso Kudu an gano wata haramtacciyar matatar mai tare da kwato lita 1000 na danyen mai yayin da aka kama mutum 25 da laifukan miyagun kwayoyi tare da hadin gwiwar NDLEA a jihohin Bayelsa da Rivers. A jihar Kaduna an kama motoci dauke da bama bamai masu nauyin kilogiram 5000 da sauran kayan hada bam.
0 Comments