Bamu Da Dalilin Shigo Da Mai Daga Ko wacce Kasa a Duniya -Dangote

Dangote

Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya bayyana cewa Najeriya tana da cikakken karfin biyan bukatun man fetur na cikin gida ba tare da dogaro da shigo da shi daga kasashen waje ba.

Fitacciya Ta rawaito cewa, Dangote ya yi wannan jawabi ne yayin ziyarar da Hukumar Raya Yankin Kudu Masu Kudu (SSDC) ta kai a Matatar Man Dangote da ke Legas.

A yayin taron, Dangote ya soki yadda wasu kamfanonin mai na kasa da kasa ke karkatar da danyen man Najeriya zuwa rassansu na kasuwanci a kasashen waje, musamman kasar Switzerland, sannan su tilasta wa matatun cikin gida sayan man a kan farashi mai tsada na karin dala hudu zuwa biyar kan kowace ganga.

Ya kara da cewa duk da Dokar Man Fetur (PIA) ta bayar da fifiko wajen samar da danyen mai ga matatun cikin gida, har yanzu ana amfani da kofofi wajen karya dokar. Ya bayyana cewa Kamfanin Mai na Kasa (NNPC) yana samar musu da danyen mai na kaya biyar zuwa shida a duk wata, amma matatar tana bukatar kaya kusan 20 a wata domin yin aiki yadda ya kamata daga watan Janairu.

Daga karshe, Dangote ya yi alkawarin samar da lita miliyan 50 na man fetur a kullum a lokacin bukukuwan karshen shekara, inda ya ce suna da shirin samar da jimillar lita biliyan 1.5 a watan Disamba na 2025 da kuma lita biliyan 1.5 a watan Janairun 2026.

Post a Comment

0 Comments