Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Yakin Neman Canja Halayen 'Yan Kasa

Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Yakin Neman Canja Halayen 'Yan Kasa
Tunibu

Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da wani sabon shiri na wayar da kan al'umma mai taken "My Nigeria, My Responsibility" da nufin farfado da ruhin kishin kasa a zukatan 'yan Najeriya.

Fitacciya Ta rawaito cewa, Ministan Yada Labarai, Alhaji Mohammed Idris ne ya kaddamar da shirin a madadin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, inda ya jaddada cewa kishin kasa ya wuce batu na baki kawai, aiki ne da ke bukatar sadaukarwa.

Shirin yana kira ga 'yan kasa da su dauki alhakin gina kasar nan ta hanyar biyan haraji, gudanar da harkoki cikin gaskiya, da kuma gujewa yada labaran karya da ka iya tayar da hankali.

A wani mataki na daban, gwamnatin ta sanar da shirin kafa cibiyar koyar da ilimin kafafen yada labarai a watan Fabrairun 2026 domin taimakawa jama'a wajen tantance sahihancin bayanai a yanar gizo.

Post a Comment

0 Comments