Gwamnatin Jigawa Ta Biya Naira Biliyan 1.8 Ga Tsoffin Ma'aikata Da Iyalan Mamata
Hukumar Fansho ta Jihar Jigawa ta raba makudan kudade har Naira biliyan 1.856 ga tsoffin ma'aikata da iyalan wadanda suka rasu su 728 a jihar.
Fitacciya Ta rawaito cewa, Babban Sakataren Hukumar, Alhaji Bilyaminu Shitu Aminu ne ya bayyana hakan a garin Dutse, inda ya ce biyan kudaden wani bangare ne na kokarin gwamnati na sauke nauyin da ke kanta ga ma'aikata.
A yayin bayar da bayanin yadda aka raba kudin, Sakataren ya ce an biya Naira biliyan 1.54 ga tsoffin ma'aikata 607, yayin da aka biya iyalan ma'aikata 96 da suka rasu Naira miliyan 289, sannan aka biya Naira miliyan 21 ga iyalan 'yan fansho 25 da suka rigamu gidan gaskiya.
Alhaji Bilyaminu ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da ba da fifiko wajen biyan hakkokin ma'aikata a kan lokaci domin inganta rayuwarsu bayan barin aiki.
Hukumar Fansho ta Jihar Jigawa da Kananan Hukumomi ta sanar da fara biyan kudaden sallama da na mutuwa da suka kai jimillar Naira Biliyan 1.856 ga tsoffin ma'aikata da iyalan mamata guda 728 a jihar.
Babban Sakataren Hukumar, Alhaji Bilyaminu Shitu Aminu, shi ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a garin Dutse, inda ya ce biyan kudaden ya shafi wadanda suka yi ritaya da kuma iyalan ma'aikatan da suka rasu suna bakin aiki.
A cikin bayanin nasa, Sakataren ya nuna cewa an ware Naira Biliyan 1.54 domin biyan tsoffin ma'aikata 607, yayin da aka ware Naira Miliyan 289 domin biyan iyalan ma'aikata 96 da suka rasu. Sannan an biya Naira Miliyan 21 ga iyalan 'yan fansho 25 da suka rasu jim kadan bayan barin aiki.
Alhaji Bilyaminu ya jaddada cewa tsarin fansho na Jihar Jigawa yana daya daga cikin mafi inganci a kasar nan, inda ya ce wannan mataki yana nuna irin jajircewar gwamnatin jihar wajen kula da walwalar ma'aikata da iyalansu a koda yaushe.
0 Comments