Gamayyar 'Yan Social Media Na PDP A Zamfara Sun Janye Yajin Aiki Tare Da Neman Afuwa
Gamayyar matasa masu tallatawa da kare muradan jam'iyyar PDP da Gwamnatin Jihar Zamfara a kafafen sada zumunta (Social Media), sun sanar da janye yajin aikin gargadin da suka shiga, tare da neman afuwar gwamnatin jihar.
Fitacciya Ta rawaito cewa, wannan mataki yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da Shugaban kungiyar, Kwamared Jamil Mohammed Labour ya fitar a ranar Laraba, 10 ga watan Disamba, 2025.
Sanarwar ta bayyana cewa sun amince su janye yajin aikin ne bayan wata tattaunawa mai fryu da suka yi da manyan jami'an gwamnati da masu ruwa da tsaki, inda gwamnatin ta nuna shirinta na duba koke-koken da suka gabatar.
Kwamared Jamil ya kara da cewa manufarsu ta shiga yajin aikin ba wai don su raina gwamnati ba ne, sai don su jawo hankalin mahukunta kan wasu matsaloli da ke ci musu tuwo a kwarya wajen gudanar da ayyukansu.
Daga karshe, kungiyar ta umarci dukkan mambobinta da su koma bakin aiki nan take, tare da fatan cewa za a ci gaba da tattaunawa har sai an warware sauran matsalolin baki daya.
"Mun Janye Yajin Aiki Kuma Muna Neman Afuwa" — 'Yan Social Media Ga Gwamnatin Zamfara
Rikicin da ya kunno kai tsakanin 'yan jaridar yanar gizo (Social Media Influencers) na Gwamnatin Zamfara da mahukunta ya zo karshe, bayan da kungiyar ta sanar da janye yajin aikin da ta fara.
Fitacciya Ta rawaito cewa, a wata wasika da Kwamared Jamil Mohammed Labour ya sanya wa hannu, kungiyar ta nemi afuwar gwamnatin jihar kan rashin jin dadin da matakin nasu ya janyo, tana mai cewa an yi hakan ne kawai don neman biyan bukata ba don yi wa gwamnati zagon kasa ba.
Bayan zama da suka yi da masu ruwa da tsaki, kungiyar ta gamsu da alkawarin da gwamnati ta yi na magance matsalolinsu, don haka ta umarci 'yan tawagar da su ci gaba da "Posting" da tallata ayyukan gwamnati kamar yadda suka saba.
0 Comments