NSCIA Ta kalubalanci Gwamnati akan ta Binciko wanda ke yada Jitajitar Kisan kan wasu Addini daya


 Nigerian Supreme Council for Islamic Affairs (NSCIA) ta roƙi gwamnatin tarayya da ta gano kuma ta fallasa mutanen da ke yada labaran ƙarya cewa ana aiwatar da kisan kiyashi akan wasu kabilu wato Kiristoci a Najeriya.

NSCIA ta bayyana cewa wasu shugabannin CAN na amfani da yada wannan jita-jitar wajen neman kuɗi da tallafi daga ƙasashen waje, suna kuma ƙoƙarin karkatar da gaskiya domin su sami goyon bayan duniya.

Hukumar ta jaddada cewa hare-haren da ake samu a ƙasar ba su takaita ga Kiristoci ba ko Musulmai, kowa na cikin waɗanda abin ke shafa, inda sama da mutane 2,200 aka kashe a Arewa cikin rabin farkon shekarar 2025, yawancinsu Musulmai.

NSCIA ta kuma nuna damuwa da yadda wasu hukumomin gwamnati ke yin shiru kan wannan batu, tana kira ga gwamnati da ta ɗauki matakin gaggawa domin kare martabar ƙasar. 

Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai. 

(Premiumtimes)

Post a Comment

0 Comments