El-Rufai Ya Yi Zargin Ana Shirin Ƙulla Masa Maƙarƙashiya Domin Ɓata Masa Suna Tare Da Cigaba Da Tsare Shi

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya nuna damuwarsa kan abin da ya kira wani ƙoƙari na alaƙanta shi da wasu miyagun ayyuka domin ganin ya jima a gidan yari, inda ya bayyana cewa ana amfani da dabarun siyasa wajen shafawa mutuncinsa kashin kaza a idon duniya.

Fitacciya ta rawaito cewa, a wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye ya fitar, ya bayyana cewa wannan yunƙuri ya biyo bayan tarnaƙin da tsohon gwamnan ya fuskanta tun a ranar 12 ga watan Fabrairun 2026, lokacin da aka yi ƙoƙarin kama shi a filin jirgin saman Abuja bayan dawowarsa daga ƙasashen waje, kafin daga bisani ya amsa gayyatar hukumomin EFCC da ICPC inda ake tsare da shi har yanzu.

Rahoton ya nuna cewa jaridar The Nation ta bankaɗo wani zargi dake nuna cewa wasu jami'an tsaro na bincikar harin da ƴan bindiga suka kai gidan wani shaida mai suna Mohammed Umar Karage, inda ake ƙoƙarin danganta lamarin da shari’ar da ake yi wa tsohon gwamnan, har ma da ambaton sunan Abubakar Idris Dadiyata wanda ya ɓace shekaru da dama da suka gabata a matsayin wani ɓangare na zargin dake kan tsohon gwamnan.

Bayanai sun tabbatar da cewa Malam Nasir El-Rufai ya ƙaryata waɗannan zarge-zarge baki ɗaya, inda ya jaddada cewa ba shi da wata alaƙa da harin da aka kai gidan Karage ko ɓatan Dadiyata, sannan ya bayyana cewa an ƙirƙiri waɗannan labarai ne kawai domin a hana shi samun beli da kuma tozarta shi a gaban ƴan Najeriya dake kallon yadda shari’arsa ke gudana.

Haka kuma, masu lura da al’amuran yau da kullum na ganin wannan takaddama a matsayin wata alama dake nuna tsanantar rikicin siyasa tsakanin tsohon gwamnan da wasu manyan ƙasaitattun mutane, duba da yadda ake ta fito da wasu sabbin zarge-zargen da ba su da alaƙa da binciken farko na karkatar da kuɗaɗe da ake yi masa a hukumance.

Masu fashin baƙi na kallon cewa dambarwar El-Rufai za ta iya shafar lissafin siyasar Arewa a zaɓen 2027, duba da yadda yake da magoya baya da kuma tasiri a cikin jam’iyyar APC, wanda hakan ya sa wasu ke ganin cewa wannan matsin lamba na da nufin raba shi da kwarjinin da zai iya amfani da shi wajen marawa wani ɓangare baya a nan gaba.

A halin yanzu, dai tsohon gwamnan ya sha alwashin ɗaukar matakin shari’a domin wanke kansa da kuma tabbatar da cewa an bi masa haƙƙinsa, yayin da magoya bayansa ke ci gaba da yin kira ga hukumomin tsaro da su bi ka’idojin shari’a wajen gudanar da bincikensu ba tare da nuna son zuciya ko amfani da siyasa ba.

Kuna ganin cewa waɗannan sabbin zarge-zargen da ake alaƙanta Malam Nasir El-Rufai da su wani mataki ne na tabbatar da adalci, ko kuwa kuna kallon hakan a matsayin wata maƙarƙashiya ce ta siyasa dake da nufin ganin bayan tsohon gwamnan?

Domin samun labarai da ɗumi-ɗuminsu, ku biyo mu a shafinmu na Facebook:
👇

Post a Comment

0 Comments