Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shigar da sabuwar ƙarar Naira biliyan 10 kan Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da sauran Laifuka, ICPC, kan zargin hana iyalansa ganinsa yayin da yake tsare.
Fitacciya ta rawaito cewa, El-Rufai ya shigar da ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/1852/2026 a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ranar 13 ga Agusta, inda ya zargi ICPC da hana matarsa, Aichatou Asabe, da ɗansa, Abba El-Rufai, ziyartarsa.
Tsohon gwamnan, ta hannun lauyansa Ubong Akpan, ya kuma haɗa Shugaban ICPC da Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya a matsayin waɗanda ake ƙara.
El-Rufai na neman kotu ta bayyana cewa haƙƙoƙin da kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya ba shi suna nan daram duk da tsare shi.
Ya zargi hukumar da hana iyalansa ganinsa domin ba shi abinci, magunguna da sauran abubuwan da yake buƙata, ba tare da wata hujja ta doka ko umarnin kotu ba.
Ya kuma yi zargin cewa jami’an ICPC sun yi amfani da ƙarfi wajen hana matarsa da ɗansa ganinsa tare da tsoratar da su a ranar 7 ga Yuli, lamarin da ya bayyana a matsayin katsalandan ba bisa ƙa’ida ba ga dangantakarsa da iyalinsa.
El-Rufai ya nemi kotu ta bayyana cewa ci gaba da hana shi ganin iyalansa ba tare da izinin doka ba ya saɓa wa kundin tsarin mulki.
Ya kuma nemi umarnin da zai tilasta wa waɗanda ake ƙara ba shi damar ganin iyalinsa da lauyoyinsa cikin sauƙi da kuma bisa ka’ida a duk tsawon lokacin da yake tsare, kamar yadda wata kotu ta riga ta umarta.
A cikin rantsuwar da aka gabatar wa kotu, Sakataren El-Rufai, Mohammed Shaba, ya ce tsohon gwamnan yana tsare ne a ofishin ICPC da ke Abuja.
Shaba ya ce matarsa ce ke kula da samar masa da abinci, tufafi, magunguna da sauran abubuwan da yake buƙata domin jin daɗinsa da lafiyarsa yayin da yake tsare.
Ya kuma bayyana cewa a ranar 1 ga Afrilu, Mai Shari’a R.M. Aikawa na Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna ya umarci ICPC ta bai wa waɗanda ake tuhuma damar ganin lauyoyinsu da kuma likitocin da suke buƙata.
Shaba ya ce wannan umarni ya nuna cewa mutanen da ake tsare da su ba za a ware su daga hulɗa da duniya ba, sannan ICPC tana ƙarƙashin kulawar kotu wajen tabbatar da yanayin tsare su.
Wannan sabuwar ƙara ita ce ta baya-bayan nan cikin jerin ƙorafe-ƙorafen shari’a da El-Rufai ya shigar kan ICPC tun bayan da hukumar ta fara bincikensa.
A watan Fabrairu, tsohon gwamnan ya shigar da wata ƙarar Naira biliyan ɗaya kan ICPC, inda ya ƙalubalanci zargin binciken gidansa da ke Abuja.
A waccan ƙarar, El-Rufai ya nemi kotu ta bayyana cewa binciken ya saɓa wa haƙƙoƙinsa na mutunci, ’yancin kai, samun adalci da kuma sirrin rayuwarsa.
Daga baya an gyara ƙarar, inda aka cire Alkalin Majistare da ya bayar da sammacin binciken daga cikin waɗanda ake ƙara.
Me Za ku ce?
0 Comments