Aƙalla mutane 32 ne ake zargin ’yan bindiga suka kashe a ƙauyen Ungushi da ke Ƙaramar Hukumar Kebbe a Jihar Sakkwato, bayan wani mummunan hari da suka kai yankin.
Fitacciya ta rawaito cewa, maharan sun kuma ƙona gidaje bakwai, shaguna biyu da motoci uku, yayin da ruwan sama ya hana gobarar yin ɓarna mai yawa, kamar yadda Aminiya ta ruwaito.
Wani shugaban ƙauyen da ya shaida harin ya ce ’yan bindigar sun shiga garin ne da misalin ƙarfe 2:15 na rana ranar Juma’a, a lokacin da jama’a ke gudanar da Sallar Juma’a.
Ya ce maharan sun ajiye babura a gaban masallaci, kafin su tarwatsa masu ibada tare da shiga cikin garin, inda suka kashe mutane biyar. Daga bisani suka sake dawowa suka kashe wasu mutane biyu, sannan suka fara harbe-harbe ta sassa daban-daban na garin.
Rahoton ya ce maharan sun ci gaba da zama a garin har zuwa misalin ƙarfe 1 na dare, kafin su tafi. Sai dai bayan wayewar gari ranar Asabar suka dawo suka ci gaba da kashe wasu mazauna yankin.
Shugaban ƙauyen ya ce da taimakon jami’an tsaro, mutanen garin sun fara neman gawarwakin waɗanda aka kashe, inda daga ƙarshe aka gano tare da binne gawarwaki 32.
Haka kuma, al’ummar yankin sun ce sun kashe ’yan bindiga 13 a yayin musayar wuta, sai dai daga baya maharan suka dawo suka kwashe gawarwakin ’yan uwansu.
Harin ya kuma shafi wasu ƙauyuka da suka haɗa da Umbutu, Maikurhuna, Gwandi, Girkau da Zugu, inda aka sace dabbobi da wasu kayayyaki masu daraja.
A wani rahoto, wani mazaunin Kebbe ya ce harin ya biyo bayan kashe sojoji huɗu a Kebbe ranar Juma’a, kafin maharan su nufi wasu ƙauyukan yankin.
Wani mazaunin Gwandi ya ce mazauna ƙauyen sun kwashe kwanaki biyu a daji ba tare da abinci ba saboda tserewa daga ’yan bindigar da suka sace dabbobinsu da sauran kayayyaki.
A nasa ɓangaren, Babban Kwamandan Rundunar Soji ta 8, Manjo-Janar Bemgha Paul Koughna, ya kai ziyara Kebbe domin duba yanayin tsaro, inda ya kuma sauya tsarin tsaro a yankin domin dakile hare-haren ’yan ta’adda da kare al’ummomin da ke cikin haɗari.
Rundunar ta buƙaci al’umma da su ƙara haɗin gwiwa da jami’an tsaro ta hanyar bayar da sahihan bayanai kan duk wani motsi ko harkar da ake zargi.
Me Za ku ce?
0 Comments