Kwankwaso ya ce Tikitin Su ya fi na Kowa kyau a zaɓen 2027


Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa haɗin gwiwarsa da Peter Obi a matsayin tikitin takarar shugaban ƙasa na 2027 ba shi da abokin hamayya wajen ƙwarewa da sahihanci.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin wata hira da Hukumar Dillancin Labaran Najeriya a Abuja ranar Lahadi.

Ya ce haɗin gwiwar nasu na da ƙarfin kayar da duk wani ɗan takara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, yana mai cewa an ƙulla shi ne domin samar da tikiti da zai haɗa ’yan Najeriya daga sassa da addinai daban-daban.

A cewarsa, tikitin ya haɗa da farin jinin Obi a Kudancin Najeriya da kuma tasirinsa na siyasa a Arewacin ƙasar, lamarin da ya ce zai samar da gagarumar ƙawance ta ƙasa baki ɗaya.

Kwankwaso ya ce babu wani tikiti da zai iya doke nasu wajen sahihanci, ƙwarewa da kuma kishin ƙasa, tare da cewa su ma sun fi sauran ’yan takara nuna tausayi ga talakawan da ke fama da matsaloli.

Ya kuma ce ƙwarewar da ya samu tun bayan zaɓen 2023 ta taimaka masa wajen fahimtar Peter Obi, lamarin da ya tabbatar masa da cewa za su iya yin aiki tare.

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa Najeriya na buƙatar sauyi sakamakon ƙalubalen tsaro, talauci, lalacewar ababen more rayuwa da matsalolin da manoma ke fuskanta.

Ya ƙara da cewa cire tallafin man fetur bai kawo sauƙin rayuwa ga ’yan Najeriya ba, yayin da manoma ke ci gaba da fuskantar matsaloli sakamakon shigo da abinci daga ƙasashen waje cikin farashi mai rahusa.

Kwankwaso ya ce haɗin gwiwar ƙungiyar Kwankwasiyya, NDC da magoya bayan Obi na da manufar kawo sauyin dimokuraɗiyya kamar wanda aka samu a shekarar 2015, bisa tsarin adalci, gaskiya da daidaito. 

Post a Comment

0 Comments