Gwamna Abba ya ce Gudanar da Mulkin Kano ba abu ne mai sauƙi ba

Gwamna Abba ya ce Gudanar da Mulkin Kano ba abu ne mai sauƙi ba
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa gudanar da mulkin jihar Kano ba abu ne mai sauƙi ba, saboda yawan al’ummarta da kuma kasancewarta jihar da ke ɗauke da mutane daga sassa daban-daban na Najeriya.

Gwamnan ya ce Kano ta zama tamkar “ƙaramar Najeriya”, saboda yawan jama’a da kuma kasancewarta cibiyar kasuwanci da zamantakewar al’umma daga sassa daban-daban na ƙasar.

Fitacciya ta rawaito cewa, Gwamnan ya bayyana hakan ne ta bakin Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Ambasada Ibrahim Waiya, wanda ya wakilce shi a taron shekara-shekara na farko na cibiyar tsaro da dabaru ta Institute of Security and Strategic Studies, ISSS.

A wajen taron, an karrama Gwamna Abba Kabir Yusuf da lambar yabo ta ƙwarewa a harkokin tafiyar da tsaro.

Gwamnan ya ce gwamnatinsa na amfani da hanyoyin tsaro na kai tsaye da kuma na sulhu wajen magance matsalolin tsaro a jihar.

Ya bayyana cewa haɗa matakan tsaro na zamani da dabarun sulhu na daga cikin hanyoyin da gwamnatinsa ke bi wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Kano.

Me Za ku ce?

Post a Comment

0 Comments