Tsaro ne ginshiƙin bunƙasar tattalin arzikin Kano - CP Bakori


Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana cewa tsaro shi ne ginshiƙin bunƙasar tattalin arziki, yana mai cewa ba za a iya samun ci gaba mai ɗorewa a fannin tattalin arziki ba tare da samar da ingantaccen tsaro ba.

Fitacciya ta rawaito cewa, CP Bakori ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi tawagar NIPSS Senior Executive Course 48 da ta ziyarci Jihar Kano, inda aka tattauna kan bunƙasa tattalin arzikin Kano, musamman fannin Orange Economy da harkokin kasuwanci.

Ya ce tattalin arzikin Orange Economy, wanda ya haɗa da masana’antun ƙirƙire-ƙirƙire, fasaha, nishaɗi, tallace-tallace da sauran sana’o’in kirkire-kirkire, na da muhimmiyar rawa wajen samar da ayyukan yi da bunƙasa harkokin kasuwanci.

Kwamishinan ya jaddada cewa dole ne hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki su haɗa hannu wajen samar da yanayin da zai ba ’yan kasuwa da matasa damar gudanar da ayyukansu cikin kwanciyar hankali.

A cewarsa, babu wata hanyar samun ɗorewar ci gaban tattalin arziki idan babu zaman lafiya da tsaro, domin tsaro yana ba da damar zuba jari, kasuwanci da samar da ayyukan yi.

Rahotannin da suka danganci jawabin sun kuma nuna cewa an mayar da hankali kan yadda tsaro zai taimaka wajen bunƙasa kasuwanci, ƙirƙire-ƙirƙire da samar da ayyukan yi a Kano.

Post a Comment

0 Comments