Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta sanar da kama mutane takwas da ake zargi da hannu wajen satar babura, tare da kwato babura shida da aka sace.
Fitacciya ta rawaito cewa, Rundunar ta ce lamarin ya fara ne bayan an kai rahoton satar babur kirar Bajaj Boxer a Ofishin ’Yan Sanda na Sabon Gari a ranar 22 ga Satumba, 2026, inda aka tura ƙarar zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na rundunar domin gudanar da bincike.
A yayin binciken ne jami’an ’yan sanda suka kama Maharazu Mohammed mai shekaru 22 da Hassan Abdullahi mai shekaru 22, dukkansu mazauna PRP Quarters a Kano.
A cewar rundunar, mutanen biyu sun amsa laifin tare da bayar da bayanan da suka taimaka wajen kama wasu mutane shida, wanda ya kai adadin waɗanda aka kama zuwa takwas.
Rundunar ta ce ci gaba da bincike da gudanar da samame ya taimaka wajen kwato babura shida da ake zargin an sace, waɗanda suka haɗa da babura Motor B guda biyu, Haojue guda uku da kuma Companion guda ɗaya.
A wani ci gaba makamancin haka, rundunar ta ce ta miƙa motoci uku da aka kwato a baya ga Asalin masu su, bayan kammala tantancewa da tabbatar da takardun mallakarsu.
Rundunar ta ce bincike na ci gaba da gudana domin gano wasu ƙarin babura da aka sace tare da kama sauran waɗanda ake zargi da kasancewa cikin wanda ake zargi da suka tsere.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya kuma yabawa jami’an binciken bisa ƙwarewarsu, tare da kira ga jama’a da su ci gaba da bai wa ’yan sanda bayanan da suka dace a kan lokaci.
Rundunar ta shawarci mutanen da aka sace wa babur da su je domin tantance waɗanda aka kwato tare da gabatar da shaidar mallakarsu. Ana iya samun ƙarin bayani ta lambar 08140081608 ko kuma a ofishin Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano da ke hedikwatar Bompai.
Me Za ku ce ?
0 Comments